Hukumar Sadarwa Ta Nijar Na Taron Tattauna Muhimman Ayyukan Watsa Labarai 

Hukumar Sadarwa Ta Nijar Na Gudanar Da Zaman Taron Tattauna Muhimman Ayyukan Watsa Labarai

Hukumar sadarwar jamhuriyar Nijar, ta kudiri aniyar samar da karin  kudaden tallafi ga kafafe yada labarai masu zaman kansu kamar yadda abin yake a wasu kasashen yammacin Afrika ta yadda za su kara inganta ayyukan watsa labarai da tsara shirye-shiryen ci gaban kasa.  

NIAMEY, NIGER - Karancin kudaden gudanarwa na daga cikin dalilan da ke mayar da hannun agogo baya a yunkurin zamanantar da kafafen yada labarai masu zaman kansu a Nijar.

Lamarin kuma yana shafuwar sahihancin shirye-shiryen da suke yadawa, matsalar da shugaban hukumar sadarwa ta CSC Salifou Labo Boucher ya fara tunanin nemar wa mafita.

Hukumar Sadarwa Ta Nijar Na Gudanar Da Zaman Taron Tattauna Muhimman Ayyukan Watsa Labarai

Kafafe masu zaman kansu daya ne daga cikin shika-shikan dimokradiya haka kuma su ke da tasiri sosai wajen fadakar da al’umma akan mahimmancin kyawawan dabi’u, saboda haka shugaban CSC ke fatan ganin sun ware lokaci na musamman don jan hankula akan maganar zaman lafiya.

A yanzu haka mambobin hukumar ta sadarwa na gudanar da zaman taronsu na wata-wata don nazarin wasu mahimman batutuwan da ke da nasaba da ayyukan watsa labarai a kasar.

Hukumar Sadarwa Ta Nijar Na Gudanar Da Zaman Taron Tattauna Muhimman Ayyukan Watsa Labarai

Jamhuriyar Nijar mai yawan al’umma million 24 na da gidajen talabijin masu zaman kansu kimanin 14 da gidajen rediyo 78 da kamfanonin jaridu 40, to sai dai wadanan kafafe na fama da karancin kudaden shiga, matsalar da a kulliyaumin ke kara ta’azzara sakamakon yanayin karayar tattalin arzikin da duniya ta tsinci kanta ciki a ‘yan shekarun nan.

Saurari Aiken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Sadarwa Ta Nijar Na Gudanar Da Zaman Taron Tattauna Muhimman Ayyukan Watsa Labarai .mp3