A kokarin karkatar da akalar tattalin arzikin Najeriya daga yadda aka saba gani zuwa ga tattalin arzikin fasahar zamani, daidai da kuduri da dabarar tattalin arzikin fasahar zamani na kasa wato NIDEPS, hukumar bunkasa fasahar zamani ta Najeriya wato NITDA tare da hadin gwiwar ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin fasahar zamani ta bude aikin gina cibiyar da ake sa ran kamalawa nan da watanni 18 domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar samar wa matasa sana’ar hannu domin su iya dogaro da kai.
Shugaba Najeriya Muhammadu Buhari, ya amince da batun gina wannan cibiyar ne a watan Nuwamban shekarar 2020, bayan amincewar majalisun kasar da samun karbuwa a taron majalisar zartarwa ta tarayya domin bunkasa tattalin arzikin kasa da samawa matasa guraben aikin yi.
Jagorar kaddamar da aikin gina cibiyar kuma ministan sadarwa da tattalin arzikin fasahar zamani, Dakta Isa ali Pantami, ya yi bayani a kan samawa matasa guraben aikin yi ta wannan kafa, yace wannan dama ce ta magance zaman kashe wando tsakanin matasa da kuma shawo kan matsalar cusa matasa aikata miyagun laifuka.
Babban daraktar kamfanin man fetur na Najeriya, Alh. Mele Kyari wanda yake daya daga cikin mahalartar taron,ya ce za su shiga a dama da su a wajen shiga jerin kasashen duniya masu tattalin arzikin fasahar zamani ta hanyar hada gwiwa da hukumar NITDA.
Shi ma babban daraktar hukumar bunkasa fasahar zamani ta Najeriya wato NITDA, Kashifu Inuwa Abdullahi, ya ce hanyar fasahar zamani ita ce ta fi inganta tattlin arziki a duniya.
A nasa bangaren, shugaban kamfanin da aka ba wa aikin ginin, Umar Abdullahi, ya ce zasu yi duk mai yiyuwa wajen gama aikin a lokacin da aka tsara.
Masu kula da lamura kamar yada malam, Kashifu Inuwa sun bayyana cewa, gina wannan cibiyar zai taimaka a kokarin mayar da tattlin arzikin Najeriya na fasahar zamani tare da rage zaman kashe wanda tsakanin matasa kuma su yi dogaro da kai.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulra’uf daga Abuja, Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5