A cikin sanarwar da shugaban gudanar da sabbin tsare tsare na kamfanin Ime Archibong ya fitar, Facebook ya bayyana cewa, ofishin da zai fara aiki a shekara ta 2021, zai kasance irinsa na farko a nahiyar Afrika da zai kunshi tawagar injiniyoyi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Bude sabon ofishinmu a Lagos zai samar da sabuwar damar bunkasa hanyoyin sadarwa na internet daga nahiyar Afrika zuwa sauran kasashen duniya. Muna ganin mutane masu baiwa da kuma kwarewa a fannin sadarwar internet a duk fadin Afrika.. bude sabon ofis din da za mu yi zai samar da damar kirkiro da ababan da zasu amfani nahiyar Afrika da kuma sauran kasashen duniya nan gaba, karkashin jagorancin ‘yan Afrika.”
Kamfanin Facebook ya fara hada hannu da kwararru a fannin fasaha a birnin Ikko a shekara ta dubu biyu da goma sha takwas kafin fadada huldar tare da bude karamar cibiyar gudanarwa da ke tallafawa kanana da matsakaitan cibiyoyin kasuwanci a nahiyar Afrika ta wajen samar da horarwa da zata taimaki ‘yan kasuwan bunkasa harkokin kasuwancinsu.
A shekara ta 2015 kamfanin Facebook ya bude ofishin shi na farko a Afrika a birnin Johanneshurg na Afrika ta Kudu da nufin tallafawa wadanda suke amfani da dandalin. Kamfanin ya kuma bayyana cewa yana taimakawa wajen bunkasa harkokin kasuwanci daga matakin kasa zuwa yanki da kuma kasashen duniya, da ya hada da tallafawa sama da kananan cibiyoyin kasuwanci 900 da annobar Coronavirus ta shafa a kasashen nahiyar Afrika.
Facebook Forum