Hukumar NAPTIP Ta Mika ‘Yan Mata Takwas Da Aka Yi Safararsu Ga Kasar Ghana

Wata mai yin karuwanci

Jami’an hukumar yaki da safarar mutane ta Najeriya NAPTIP ta mikawa jami’an diplomasiyyar Ghana wasu ‘yan mata takwas da aka so yin safararsu zuwa kasashen Larabawa.

‘Yan Matan guda takwas wadanda dukkanninsu ‘yan kasar Ghana ne, sun shiga hannun jami’an shige da fice na Najeriya a filin saukar jirage na Murtala Muhammed dake birnin Lagos, aka kuma mika su ga hukumar NAPTIP.

Bincike da hukumar NAPTIP ta gudanar an gano cewa ‘yan matan wadanda shekarunsu ya kama daga 24 zuwa 34 ‘yan aikatau ne. Domin shida daga cikinsu a baya sun yi aikatau a kasashen Kuwait da Dubai da Saudiyya kafin daga bisani a mayar da su gida Ghana.

Haka kuma hukumar ta gano cewar an shigo da ‘yan matan ne daga kasar a Ghana, da nufin tafiya da su kasar Misira ta jirgin Egypt Air, daga can kuma a kaisu Kazakhstan don aikatau.

Gano hakan ne ya sa mahukuntan Najeriya suka tsare ‘yan matan aka kuma mikasu ga jami’an diplomasiyyar Ghana dake Najeriya don mayar da su gida.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar NAPTIP Ta Mika ‘Yan Mata Takwas Da Aka Yi Safararsu Ga Kasar Ghana - 2'26"