Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Borno: Rikici Na Neman Kunno Kai a Jam’iyyar APC


BORNO: Zaben APC
BORNO: Zaben APC

Da alamu wata sabuwar rigima ce ke kokarin kunno kai a tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a jihar Borno, sakamakon zaben fidda gwani da aka yi a makon jiya.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC dai sun nuna kin amincewarsu da sakamakon zaben, har ma suka nemi a rushe zaben da suka kira nadi.

Irin wannan tayar da jijiyoyin wuyan dai na ci gaba da gudana ne tun bayan da kammala zaben fidda gwamni na kujerar gwamnan jihar Borno, inda aka samu ‘yan takara 21 dake neman kujera daya tilo, wanda daga bisani gudan 10 suka janye.

‘Yan takarar 10 da suka janye sun marawa Farfesa Babagana Umara Zulum, wanda tun farko gwamnan jihar ya bayyana shi a matsayin dan takararsa. Sai dai wasu daga cikin ‘yan takarar sun nuna kin amincewarsu da sakamakon zaben, har ma suka nemi jam’iyyar APC ta rushe zaben.

Karamin ministan ayyuka na tarayyar Najeriya, Mustapha Baba Shehuri, wanda ya kasance cikin ‘yan takarar 21, ya ce babban abin da ya daure masa kai shine yadda aka baiwa kowanne wakili Naira dubu dari biyu biyu, ganin yadda wasu mutane ke cikin wahala a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Wakilin Muryar Amurka ya zagaya ma’aikatar kananan hukumomi da ake zarginb cewa an fitar da wadannan kudade, sai dai babu wani jami’i da yayi magana suna mai cewa kwamishina ne kadai zai iya yin magana, amma kuma yanzu haka babu kwamishinoni biyo bayan soke su da aka yi makonni biyu da suka gabata.

Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG