Shugaban asusun kula da yawan al'ummar Afrika na Majalisar Dinkin Duniya Mabingue Ngom, yace ya zama wajibi a kula da rayuwar yara mata ta hanyar basu ilimi mai inganci da tarbiyya, mutukar ana so a raya nahiyar Afrilka. Mr. Ngom yayi wannan kiran ne a wani taro da aka gudanar a ranar 11 ga wata Satumbar 2018 a Abuja.
Ya kuma nuna damuwa ga yadda ake nuna halin ko in kula ga rayuwar yara mata a nahiyar. Taken taron shine gudunmawar shuwagannin addinin musuluunci wajen karfafa hanyoyin dogaro da kai ta bangaren matasa maza da mata.
Sarkin Shanga, wanda ya wakilci Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar a taron, ya bayyana yadda yawan matasa da magidanta marasa aikin yi yayi katutu a Najeriya, da kuma yadda hakan ke kawo wa kasar koma baya.
Ga Hauwa Umar da karin bayani...
Your browser doesn’t support HTML5