Hukumar Leken Asiri Ta Amurka Ta Fitar Da Wasu Tsaffin Bayanan Sirri

Hukumar leken asirin tsaron ‘kasa ta fitar da wasu tsoffin bayanan sirri da aka baiwa tsoffin shugabannin Amurka Richard Nixon da Gerald Ford, a lokacin mulkinsu shekara ta alif 970 wanda ke karin haske kan yadda lokacin yakin cacar baka ta kasance a duniya.

Cikin kundin mai shafuka 28,000 akwai bayanai masu ban mamaki kan kasashen duniya, ciki har da yakin Vietnam mai cike da sarkakiya da yayi sanadiyar rasa rayukan sojan Amurka sama da 58,000.

An dai baiwa shugaba Nixon da Ford na wancan lokacin, an kuma kwafarwa fadar shugaban kasa tsawon shekaru 8 tun daga ranar 20 ga watan Janairu shekara ta 1969. Cikin bayanan akwai ziyarar Xixon zuwa kasar China da Tarayyar Soviet mai cike da tarihi, wadda itace ziyarar da shugaban Amurka ya taba kaiwa.

A bayanan da aka baiwa Ford a shekarun mulkinsa, akwai abubuwan ci gaba kamar kawo karshen yakin Vietnam, sai kuma mutuwar shugaban kasar China na farko Mao Zedong.