A taron masana sun tattauna kan yadda za a kawo karshen annobar Kwalara a kasashen. Daya daga cikin kwararrun da suka wakilci Najeriya a taron daraktan ma’aikatar lafiya Dakta Nasiru Sani Gwarzo, yace a kwai matakai da aka yanke tsakanin kasa da kasa wanda ake kira Cross Border.
Kasancewar a baya idan an sami wata annoba ta bullo akwai wasu matakai masu tsawo da mutane ke bi kafin daga karshe ta kai ga hukumar WHO, amma yanzu an yanke shawarar cewa a karfafa kwamitin ma’aikatan dake bakin iyaka domin tabbatar da ganin an dakile yaduwar cutar.
Duk da yake kusan duk shekara sai an sami bullar annobar Kwalara a yawancin kasashen. Tsaftace muhalli da abinci kadai ake bukata wajen kawar da annobar inji Nasiru Sani Gwarzo, yace kuma kusan duk fadin duniya babu inda annobar Kwalara tayi katutu irin kasashen Hudu na tafkin Chadi.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5