Tuni dai hukumar Kwastam ta hana shigowa da motoci ta kan iyaka sai ta tashohin ruwan Najeriya, a wata sanarwa da hukumar da fitar wanda kakakinta Joseph Atta, ya rattabawa hannu, wadda ke cewa matakin da hukumar ta dauka na kumshe ne a karkashin dokar hukumar, sashe na 147.
Sai dai kuma masu sayar da motoci a Nageriya, sun fara kokawa dangane da samamen da hukumar ta kwastan ke kaiwa a ofisoshi da shagunan su ko kuma wuraren da suke sayar da motoci, inda suka zargi hukumar da musguna masu.
Alhaji Mohammed Ali, shine babban kwantirola mai kula da shiyyar Seme-Boda, dake kan iyakar Najeriya, da Benin, kuma ya bayyana cewa dalilin kama mota shine domin tantance takardun rajistar mota, dan haka suna bin Kadin tsarin hukumar ne.
Ko a farkon watannan da muke ciki hukumar ta kama wasu motoci goma sha daya na alfarma da aka kyasta kudin su ya kai Naira miliyan dari da ashirin da biyar da lugo hudu, da suka hada da motoci kirar Lexus Jeep, da Toyoya, da Marsandi da manyan motocin daukar kaya.
Mohamed Uba, shine kwantirolan hukumar dake kula da shiyya ta daya ya bayyana cewa dalilin daya sa suka kara kaimi shine domin shigowa da makamai da ake yi a kasar.
Domin karin bayani saurari rahoton Babangida Jibrin daga Legas.
Your browser doesn’t support HTML5