Yau ne rana da ya kamata Shugaban kungiyar ‘yan aware na IPOB Nnamdi Kanu, ya baiyana a gaban kotu domin cigaban Shari'ar da ake yi tsakanin kungiyar da Gwamnatin Tarraiyya Amma bai zo kotun ba.
Hayaniya ta auku a kotun tarayya Abuja inda mai shara’a Binta Nyako, tayi zama domin ci gaba da shara’a tsakanin gwamnatin tarayya da haramtacciyar kungiyar yan aware ta IPOB wanda Nnamdi Kanu ke shugabanta.
Bayan an kwashi tsahon lokaci har na awa uku, Nnamdi bai bayyana a kotun ba lauyansa Ifeany Ejofo yace akwai damuwa.
Ya kara da cewa ya shedawa kotun cewar dole ne shugaban rundunar Sojojin Nigeria Tukur Yusuf Burutai, da ya fito dashi domin tun ranar da Sojoji suka kai sumame gidan Kanu, a ranar 14, ga watan jiya kawo yanzu bai sake sanin inda Kanu, yake ba.
Lauyan gwamnmati Shuaibu Labaran, ya nemi a daga shari’ar domin lauyan sa bazai iya gabatar dashi ba. Akwai wadanda sukayi belinsa kamar senator Abaride, yace yanada hakki ya kawo shi gaban kotu in kuma indan har baya so ya ci gaba da kasancewa wanda ya tsayawa Nnamdi Kanu, sai ya gayawa kotu ta cireshi daga mai tsaya masa. Kotun ta daga sharia zuwa sha hudu ga watan gobe.
Facebook Forum