Shugaban Najeriya, Muhammad Buhari ya yi alkawari inganta rayuwar al’ummar Niger Delta ta fannoni daban daban.
Shugaban ya ba da tabbacin hakan ne yayinda yake sa hannu a kudurin wata dokar kafa Jami’ar nazari akan albarkatun man fetur da za’a kafa a Effurun dake kusa da Warri a jihar Niger Delta.
A hirar da wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa ya yi da wani malamin Jami’a, Dr. Usman Muhammad dangane da mahimmancin jami’ar, malamin yace yana ganin kafa jami’ar a yankin Niger Delta ba zai kwantar masu da hankali ba. A zahiri ma suna iya fitowa da wata fitinar tare da wasu bukatu saboda ta dalilinsu akan yi watsi da cibiyar ilmin man fetur da aka kafa a Kaduna.
Shi ko Farfesa Almustapha Ujudu gani yake wannan sabuwar jami’ar zata rage yawan kashe kudi zuwa kasashen waje neman ilmin.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani
Facebook Forum