Hukumar kwallon kafa ta kasar Ingila tana bukatar Kocin kasar Gareth Southgate, ya cigaba da Jan ragamar kocin ‘yan Ingila har gaba da shekarar ta 2020.
Kocin mai shekaru 47 a duniya wanda ya karbi ragamar aiki a hannun Sam Allardyce, a shekarar 2016 bisa yarjejeniyar kwantirakin shekaru hudu, a zuwansa ya taimakawa kasar inda takai matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin duniya da aka kammala na 2018 a kasar Rasha, kuma Rabonta da wannan mataki tun kimanin shekaru 28 da suka wuce.
Shugaban hukumar kwallon kafa Martin Glenn, ya ce bisa la'akari da wanna namijin kokari suke bukatar Kocin ya ci gaba da Jan ragamar kungiyar har bayan karewar kwantirakinsa a shekarar 2020 inda za'a kara tsawaitata domin muna kaunar da ake ma sa.
Manchester United, tana yunkurin tayi kan dan wasan baya na Barcelona, Yerry Mina, dan shekaru 23, a duniya dan kasar Columbia bayan da ta rasa samun sayen dan wasan baya na Leicester city Harry.
Tottenham zata sanya fam miliyan 35 wajan sayen dan wasan tsakiya na Bournemouth mai suna Lewis Cook, mai shekaru 21 wanda ya rike Kaftin a tawagar ‘yan kasa da shekaru 20 na kasar Ingila a gasar cin kofin duniya na matasa da ya gabata.
Alamu na nuni da cewar Chelsea za ta shiga hatsarin rasa mai tsaron ragar BelgiumThibaut Courtois mai shekaru 26 a kan kyauta idan har ba za su iya daukar wanda zai maye gurbinsa kafin a rufe hada hadar ‘yan wasa a ranar 9 ga watan Agusta, ba.
Dan wasan tsakiya na Real Madrid, da Croatia Mateo Kovacic, dan shekaru 24, da haihuwa ba zai koma kungiyar Manchester United ba saboda bai da sha'awar ya buga wasa a karkashin jagorancin mai horas da kungiyar Jose Mourinho.
kungiyar Bayer Leverkusen, ta tuntubi Tottenham a kan dan kwallon tsakiyarta Marcus Edwards, mai shekaru 19, domin batun dawowarsa gareta.
Kungiyar Westham ta yi tayin fam miliyan 17 kan dan wasan gaba ba Celta Vigo, dan kasar Uruguay, mai suna Maxi Gomez, sai dai kungiyarsa taki amincewa inda take bukatar fam miliyan 35 kafin acimmna yarjejeniyar dan wasan mai shekaru 21 a duniya.
Daraktan fasaha na kungiyar Barcelona, Eric Abidal, ya musanta rade radin da ake yi na cewar ya tuntubi dan wasan tsakiya na Manchester united, Paul Pgoba, kan batun dawowarsa kungiyar ta Barcelona.
Bayanai na nuni da cewa komai ya kammala kan komawar dan wasan gaba na Juventus, Gonzalo Higuain, dan shekaru 30, zuwa kungiyar AC Milan a matsayin rance bisa yarjejeniyanr saye nan gaba wadda ake alakantashi da kungiyar Chelsea.
Har ila yau kungiyar ta AC Milan tana zawarcin wani dan wasan da Chelsea take nema daga kungiyar Juventus, mai suna Mattia Caldara, dan shekaru 24 a duniya.
Your browser doesn’t support HTML5