Hukumar Kula Da Wayar Salula Ta Gargadi Wasu Kamfanonin Waya A Najeriya

  • Ladan Ayawa
Hukumar kula da kamfanonin wayar salula a Nigeria ta gargadi kamfanonin dake boye lambobin da ake kira daga kasashen waje da su daina, ko kuma su hadu da hushin hukumar

Hukumar kula da kampanonin sadarwa a Najeriya ta koka akan yadda wasu kamfanoni ke boye lambar masu bugo waya cikin kasar daga kasashen waje.

Suka ce suna haka ne da niyyar samun ribar da ya wuce na wanda ya kamata su samu. Hakan na iya kawo barazana ga harkar tsaro da kuma kawo koma baya ga harkar sadarwa.

Akan haka ne hukumar ta gayyaci wasu kamfanoni biyu wadanda akace sunyi kaurin suna wurin wannan tabiaar.

Hukumar taja kunnen su kuma tayi alkawarin hukunta duk wata kanfani data samu da aikata wannan tabi’a.

Sai dai wasu ‘yan Najeriya sunce ba gargadi kawai ba, hukumar kula da harkokin salulan ta tabbatar tabi kalaman ta a aikace ba wai gargadi na fatar baki ba.

Ga Nasir Adamu El-Hikaya da karin bayani.2'59

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kula Da Wayar Salula Ta Gargadi Wasu Kamfanonin Waya A Najeriya