Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yi Taron Inganta Tsaro a Najeriya


Idris Ibrahim-Sufeto Janar Yan Sanda a Najeriya
Idris Ibrahim-Sufeto Janar Yan Sanda a Najeriya

Ministan Harkokin Cikin Gida a Najeriya Abdurrahaman Danbazzau da takwaransa na Ma'akatar Noma Audu Ogbeh sun yi wata ganawa da wasu Gwamnonin jihohi shida da sauran masu ruwa da tsaki a kan batutuwa da suka shafi harkar tsaron kasa.

Gwamnonin da suka halarcin zaman sun hada da na jihohin Neja, Kaduna, Taraba, Nasarawa, Binwai, da kuma Adamawa. Ko bayansu akwai Sufeto Janar na 'Yansanda, da shugaban Ma'aikatar Tsaro na farin Kaya, da Shugaban Hukumar Leken asirin kasa. Kusoshin tsaron sun kwashe sa'o'i kimanin bakwai suna nazarin hanyoyin magance matsalolin tsaro dake damuwar kasar.

Mahalarta taron sun amince cewa za horar da jami’an tsaro na musamman wanda za a kirasu “Agro Rangers” da yawansu zai kai dubu biyar da nufin sa ido a duk rikicin da ake yi a dazuzzukan kasar. Ministan Harkokin Cikin Gida Dambazau ya yiwa wakiliyarmu Madina Dauda karin haske inda ya tabbatar mata da cewa, tuni aka zabo wadannan jami’an tsaro dubu biyar ana jiran kudi ne kawai aje a horar da su a kan aikin da za su yi.

Shima gwamnan jihar Taraba Darius Dickson Ishaku yace jihar na kokarin hana kiwo kuma ya kare dokar da ya kafa dangane da kiyo a jihar, inda yace dokar ba zata cutar da kowa ba kuma hukuma zata samarwa makiyaya ciyawa da ruwa da zasu yi anfani da su wajen kula da dabbobinsu.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG