Babban sakataren kungiyar Waziri Ideo, ke bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Mr Waziri, ya bayyana cewa ya kamata gwamnati ta yi tambaya akan wadannan manyan kudade, ya kamata hatta gwamnatocin jahohi su shiga maganar domin gwamnatin tarayya da jihohi har ma da kananan hukumomi su samu nasu kaso.
Kamfanin Gas, wato LNG, ya biya kamfanin NNPC wadannan makudan kudi amma ya ki sa kudin a asusun gwamnatin tarayya kamar dayya kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya, ya tsara. Ko menene dalilin da yasa wannan hukuma ke fitar da wadannan alkaluma a yanzu?
Tambayar da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Hassan Maina Kaina, ya yiwa sakataren kungiyar Kenan, wanda ya kada baki ya bayyana cewa suna kokarin nuna wa gwamnati inda zata sami kudi ne, domin akwai bukatar su a Najeriya.
Malam Yusha’u Aliyu, masanin tattalin arziki ne a Najeriya, ya bayyana cewa kudaden da wannan hukuma ke nema manyan kudade ne wanda sun fi kasafin kudin bana da aka yi, kuma kudade ne da aka samesu tun darajar kudaden waje basu kai darajar da suke da ita a yanzu ba.
A cewar shugaban rundunar adalci ta Najeriya, Alhaji Abdulkarim Dayyabu, wannan kudade basu bashi mamaki ba domin tun lokacin da tsohon shugaba marigayi Janar Abacha, ya kafa wani kwamiti, aka fara maganar kudi Dala Miliyan Dubu Goma sha Biyu da Dari biyu da aka fitar na Mai amma ba’a shigo da kudin ba da sauransu
Daga Abuja ga rahoton Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5