Hukumar Kula Da Hakar Albarkatun Man Fetur Ta Najeriya Zata Mayar Da Wasu Ofisoshinta Zuwa Legas

NUPRC

Hukumar kula da hakar albarkatun man ta Najeriya (NUPRC) na duba yiyuwar mayar da wasu daga cikin ofisoshinta daga Abuja zuwa Legas, a cewar wata sanarwar da Dr. Kelechi Onyekachi Ofoegbu ya fitar a madadinta.

Sanarwar tace an yanke shawarar ne da nufin inganta ayyukan hukumar da rage yawan kudaden da ake kashewa wajen gudanar da ayyuka tare da yin amfani da kadarorinta dake Legas yadda ya dace.

Sanarwar na cewa, “a bisa dacewa da manufofinmu na inganta ayyukan hukumar NUPRC da bunkasa harkar hakar man fetur tare da alkinta ofisoshinmu dake Abuja yadda ya dace, muna duba yiyuwar mayar da wasu bangarorinmu zuwa Legas.”

“Bukatar inganta ayyukanmu da rage kashe kudaden gudanarwa tare da cin gajiyar gine-ginenmu dake Legas yadda ya dace ne suka sabbaba wannan tunani.”

“Sakamakon haka, muka bukaci kowane bangare ya tantance tare da fitar da sunayen ofisoshin da zasu iya tsayawa da kafafuwansu a fannin tafiyar da ayyuka karkashin karamar kulawa.”

“Ana sa ran samun sunayen irin wadannan bangarori kafin ranar juma’a 23 ga watan febrairun da muke ciki.”

Wannan al’amri na zuwa ne bayan dauke shelkwatar Hukumar Kula da Filayen Jiragen Saman Najeriya (FAAN) da ga Abuja zuwa Legas tare da mayar da wasu ofisoshin Babban Bankin Najeriya zuwa birnin Ikko; cibiyar kasuwancin Najeriya.