Hukumar Kiyaye Ibtila’i Da Ba Da Agaji A Ghana Ta Kaddamar Da Atisayen Kwana Uku

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo

Bayan taron bita na mako guda domin shirye-shiryen ko-ta-kwana a kan girgizar kasa da Hukumar Kiyaye Ibtila’i da bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NADMO) tare da haɗin gwiwar Rundunar Tsaro ta Arewacin Dakota, da kuma Ofishin Jakadancin Amurka, an ƙaddamar da atisayen kwanaki uku a hedkwatar NADMO

ACCRA, GHANA - Biyo bayan rawar kasa da aka samu a kasar kwanan nan, gwamnatin Ghana ta hanyar hukumar kiyaye ibtila’i da ba da agajin gaggawa ta kasa (NADMO) ta dora wa masu ruwa da tsaki alhakin tabbatar da hadin gwiwa mai dorewa don dakile ko rage tasirin ibtila’i, musamman na girgizar kasa a kasar.

Ko da yake Ghana ba ta kusa da manyan yankunan girgizar kasa na duniya, duk da haka, ta fuskanci bala'in a baya tun a shekarar 1636. Mafi girma a cikinsu su ne wadanda akayi a shekarun 1862, 1906 da kuma 1939.

Wacce aka yi a ranar 22 ga Yunin 1939, mai karfin 6.5 a ma’aunin Richter ce mafi muni, domin mutane 17 sun rasa rayukansu sannan 133 suka jikkata. Mafi kusa shi ne wanda ya faru a ranar 24 ga watan Yunin 2020 da unguwanni da dama a Accra suka jijjiga.

Domin shirye-shiryen ko ta kwana, hukumar NADMO da hadin gwiwar Rundunar Tsaro ta Arewacin Dakota, da kuma Ofishin Jakadancin Amurka, aka kaddamar da cikakken atisaye na kwanaki uku a hedkwatar hukumar NADMO dake Accra.

Da yake jawabi a wajen taron manema labarai kan atisayen, domin wayar da kan jama’a kan matakan kariya idan ibtila’in ya faru, babban darektan hukumar, Eric Nana Agyeman-Prempeh ya yi korafin rashin isassun budaddun filaye da mutane za su hadu idan girgizar kasa ta faru. Domin haka ya yi kira ga wadanda abin ya shafa da su yi wani abu a kai.

“Ina kira ga majalisun manyan birane da gundumomin da su yi duba na basira su daina cike sauran filayen da suke akwai da gine-gine kuma su kirkiro wasu filayen da mutane za su fake, ba a Accra kadai ba amma duk fadin kasar”, a cewar babban darektan.

Ya kuma kara da cewa filaye da aka yi tanadi don wasanni, musamman a makarantu, an mayar da su filayen kwallo na zamani.

Manjo Jarrod Simek na ofishin jakadancin Amurka mai kula da harkokin tsaro ya bayyana farin cikinsa a kan shirye-shiryen da aka yi. “Matakin shirye-shirye tsakanin Ghana da tawagar da muka aiko daga arewacin dakota domin su taimaka a wannan atisayen, ina jin wanka za ta biya kudin sabulu a kwanaki masu zuwa”. Ya kuma nanata bukatar a hada hannaye don shirya yadda ya kamata ga duk wani bala'i na gaggawa a nan gaba.

Baya ga hukumar NADMO da rundunar tsaro ta arewacin Dakota, dakarun soji na Ghana, hukumar motocin daukar marasa lafiya na kasa, hukumar kwana-kwana ta kasa, hukumara lafiya ta kasa da kuma hukumar ‘yan sanda Ghana duka suna tallafawa wajen tabbatar da wannan atisaye.

Saurari rahoto cikin sauti daga Idris Abdullah Bako:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kiyaye Ibtila’i Da Bada Agaji A Ghana Ta Kaddamar Da Atisayen Kwana Uku Akan Girgizar Kasa.MP3