Hukumar Kididdiga Ta Ce An Rage Haihuwa A Nijar

Taron Fadakar Da Mata Tasirin Tsarin Iyali A Ranar Mata Ta Duniya.

Hukumar kididdigar jamhuriyar Nijer ta bayyana gano raguwar haifuwa a kasar sakamakon yadda jama’a su ka fara amincewa da matakan tsarin iyali.

Sai dai a daya bangare mutuwar yara ‘yan kasa da shekara daya da haifuwa ta karu saboda haka hukumar ta shawarci mahukunta akan bukatar gudanar da bincike domin gano zahirin dalilan da ke haddasa wannan matsala.

A binciken da tace ta gudanar daga shekarar 2019 zuwa 2021 hukumar kididdiga ta kasa wato INS a rahoton da ta gabatar a yayin wani bukin musamman tace an samu ci gaba sosai a yunkurin ganar da jama’a mahimmancin shimfida tsarin iyali a Nijer idan aka kwatanta da yanayin da ake ciki a shekarar 2012.

Hukumar ta INS na danganta wannan al’amari na mace macen yara kanana da wasu tarin dalilai. Jami’in hukumar kididdiga Ouseini Lamou youssoufa ya zayyana abinda suka gano a game da wannan al’amari. A cewarsa a lokacin aka yi kiddidiga, an yi shi lokacin covid-19, lokacin al'umma ba su samu zuwa wurin likita ba, don haka yawanci yara ba su samu rugakafin ba. Yanzu haka suna so su bincika dalilin da su ka sa yara ke mutuwa kafin su kai shakara guda.

Ku Duba Wannan Ma UNFPA, Hukumar Kula Da Yawan Jama'a A Najeriya Sun Nuna Damuwa Kan Mace-mace Sanadiyyar Daukan Cikin Da Ba A Shirya Masa Ba

A wani abinda ke zama ci gaba a yunkurin fadakar da jama’a rashin dacewar aurar da ‘yan matan da ba su kosa ba bincike ya gano raguwar wannan dabi’a da masana suka ayyana a sahun wadanda ke barazana ga rayuwar yaran da aka yiwa auren wuri.

Sauarari cikakken rahoton cikin sauti :

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Kididdiga Ta Ayyana Gano Raguwar Haifuwa A Nijer