ABUJA, NIGERIA - Biyo bayan zargin kare hakkin dan Adam, ciki har da zubar da ciki ga mata fiye da dubu goma da mayakan Boko Haram suka yi wa fyade, da ake zargin rundunar sojojin Najeriya da aikatawa, yanzu dai hukumar kare hakkin dan Adam ta Najeriya ta kaddamar da bincike.
Da yake kaddamar da kwamitin binciken a Abuja, Shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta Najeriya, Mr. Anthony Ojukwu, ya ce yana da Keaton gwiwa kwamitin zai yi aiki tukuru don binciko gaskiyar lamarin.
Mr. Ojukwu ya ce alhakin wannan kwamitin shi ne binciko gaskiyar zarge zargen da ake wa rundunar sojin Najeriya na danne hakkin dan Adam kamar dai yadda wani rahoton kamfanin dillancin labaru na Reuters ya nuna.
Kwamitin kazalika zai karbi takardun Korafi daga hannun daidaikun jama’a da kungiyoyin fararen hula na Arewa maso gabas. Don a tantance ko an Tafka aika aikar yi wa 'yancin dan Adam karan tsaye don sanin wa za a dora wa alhakin hakan, kana a duba yiwuwar biyan diyya ga wanda aka yi wa ba daidai ba.
Shugaban kwamitin mai shari’a Abdu Aboki ya nanata kudirinsu na yin aiki Bil hakki da gaskiya don gano gaskiyar me ya faru.
“Aikinmu shine yin bincike don ganin hakikanin abin da ya faru na zargin cin zarafin dan Adam kamar dai yadda rahoton na REUTERS ya nuna” Inji Justice Abdu Aboki.
Tuni kuma masu fafutika a Najeriya irinsu Barrister YAKUBU Sale Bawa dake zama Lauyan tsarin mulki wanda ke cewa ya zama wajibi a yi bincike don gano abin da ya faru.
Barrister Bawa ya ce kare hakkin bil’adama wani Sinadari ne cikin shika shikan dimokradiyya, yana mai cewa za su sa ido don tabbatar da an bankado abin da ya faru.
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam a Arewa maso gabas irinsu Mojin na cewa wannan yunkuri abin a yaba ne. Kamar yadda shugabanta Zakare Adamu ke cewa.
Malam Zakare ya ce tun farko dai sakacin gwamnati ne ya haddadasa duk wannan rudani kasancewar ta gaza bincikar musabbabin abin da ya janyo aukuwar rikicin na Boko Haram da yanzu ya haifar da wannan illa.
Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:
Your browser doesn’t support HTML5