Hukumar FIFA Ta Ci Najeriya Tarar Dala 154,128

FIFA

Hukumar ta dauki wannan matakin ne bayan wani hargitsi da aka samu a lokacin da Najeriya ta kara da Ghana a wasan neman shiga gasar kwallon ƙafa ta duniya a watan Maris.

Abuja, Najeriya - Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ta bayyana cin tarar Najeriya ta kuɗi da suka kai Dala dubu ɗari da hamsin da huɗu da ɗari ɗaya da takwas saboda hatsaniyar da aka samu a babban filin kwallon ƙafa na birnin tarayya Abuja a lokacin da tawagar kwallon kafar ƙasar ta fafata da takwararta ta Ghana.

An sami hatsaniyar ce a yayin wasan neman shiga gasar kwallon ƙafa ta duniya tsakanin Najeriya da Ghana a ranar ashirin da tara ga watan Maris na wannan shekarar ta 2022.

Kwamitin ladabtarwa na FIFA ya ce an sami rashin cika sharruɗan tabbatar da tsaro a filin wasan, wanda ya kai ga 'yan kallo jefe wa 'yan wasa robobi tare da shiga filin wasa.

Hukumar ta FIFA dai ta ci tarar wasu ƙasashe da dama kan laifuffuka daban-daban.