Hukumar FBI Ta Gano Wanda Ya Aikewa Obama Sakon Bam

Shugaba Barack Obama.

Hukumomi a Amurka sun ce an kama wani mutumin da aka dade ana samunsa da aikata laifuka a jihar Florida a jiya Juma’a, kuma an same shi da aika akalla kunshi 13 masu dauke da abubuwar fashewa zuwa ga masu sukar lamirin shugaba Donald Trump.

Antoni Janar Jeff sessions ya fadawa manema labarai cewa an caji Cesar Sayoc mai shekaru 56 da haifuwa a Aventura dake Florida da laifukan tarayya guda biyar, ciki har da aikewa da abubuwan fashewa ta barauniyar hanya da kuma yiwa jami’an gwamnati barazana. Ya kara da cewa Sayoc zai iya huskantar hukuncin dauri na tsawon shekaru 48 a gidan yari.

An aike da bama-baman ne zuwa ga tsohon shugaba Barack Obama da kuma wasu jiga-jigan jami’iyar Democrat ciki har da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton da tsohon Antoni Janar da wakilan majalisa na Democrat su biyu da kuma tsohon babban jami’in hukumar leke asirin Amurka John Brennan.

Darektan hukumar binciken manyan laifuka ta FBI Christopher Wray ya fada a taron manema labarai cewa wannan ba batu ne na karya ba, sai dai ya kuma ce babu wani bam da ya tashi.

Hukumomi sun fadawa kamfani dillancin labarai na Associated Press cewa ba a shirya bama baman ta yanda zasu fashe ba a lokacin da aka bude kunshin, sai dai sun ce basu iya ganewa ba ko wanda ya shirya bama baman ne bai iya ba ko kuma ba a shirya da nufin barna ba.

An dai samu hoton yatsu ne a kan kunshin da aka gano, lamarin da ya kai ga binciken Sayoc.