Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Zakulo Wadanda Suka Aika Sakonnin Bam - Trump


Shugaban Amurka Donald Trump yayin da yake tsokaci kan sakonnin bam da aka aikawa wasu manyan tsoffin jami'an gwamnati.
Shugaban Amurka Donald Trump yayin da yake tsokaci kan sakonnin bam da aka aikawa wasu manyan tsoffin jami'an gwamnati.

Trump ya ce za a kaddamar da wani babban bincike karkashin gwamnatin tarayya domin zakulo wadanda ke da hannu a aikawa da wadannan sakonni na bam.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi Allah wadai da wasu sakonni da aka aikawa wasu manyan tsoffin jami’an gwamnati dauke da bam, yana mai kwatanta lamarin a matsayin abin “kyama.”

Trump wanda ya nuna “tsananin bacin ransa”, ya kara da cewa Amurka ba ta da hurumin irin wannan dabi’a, yana mai cewa bai ji dadi da aukuwar wannan lamari ba.

Sakonnin na bam an aika su ne ga tsohon shugaban kasar Barack Obama da kuma abokiyar hamayyarsa a zaben 2016 Hillary Clinton.

Har ila yau an aike da makamancin wadannan sakonni na bam ga tsohon Attorney Janar din Amurka, wanda dan majalisa ne karkashin jam’iyar Democrat da kuma tsohon Darektan hukumar leken asiri a Amurka ta CIA, wadanda duk masu yawan sukan shugaba Trump ne.

Trump ya ce za a kaddamar da wani babban bincike karkashin gwamnatin tarayya domin zakulo wadanda ke da hannu a aikawa da wadannan sakonni na bam.

“Tabbatar da lafiyar Amurkawa, shi ne muhimmin abu a gare ni.” Inji Trump

Baya ga wadannan mutane, an aikawa da ofishin yada labarai na CNN da ke birnin New York irin wannan sako mai dauke da bam.


Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG