Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka tana gudanar da bincike kan Jared Kushner, sirikin shugaban Amurka Donald Trump kuma babban mai bashi shawarwari, akan yiwuwar hulda tsakanin ofishin yakin neman zaben Trump da Rasha, bisa ga rahotannin jaridar Washington Post da kuma NBC jiya alhamis.
WASHINGTON D.C. —
Sa ido kan Kushner da hukumar FBI ke yi ba yana nufin tana tsammani ya aikata laifi ba, ko kuma hukumar tana daukarshi a cikin wadanda take bincike game da Rasha.
Masu gudanar da binciken suna bibiyar ganawar da Kushner ya yi da jakaden Rasha Sergey Kislyak da kuma wani shugaban bankin Rasha karshen shekarar da ta gabata yayinda ake shirin mika mulki, bisa ga rahoton Washington Post.
Makon da ya gabata, jaridar ta buga rahoto cewa, ana bincike kan wani babban jami’in fadar White House dake kusa da shugaban kasa, duk da yake bata ambaci sunan Kushner ba a lokacin.