Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Damke Wasu Mutane Biyu A Wani Samame Da Aka Kai A Birnin Manchester


Yan Sandan Birtaniya
Yan Sandan Birtaniya

A cigaba da binciken da ake yi a Manchester dake Birtaniya Yan Sanda sun kama Kimanin mutane Takwas.

A yanzu haka, ana rike da mutane 8 dangane da harin bam na kunar-bakin-wake da aka kai lokacin wasan wata mawakiya a birnin Manchester na kasar Ingila, ciki har da wasu mutane biyun da aka damke a lokacin sumame yau alhamis.

An kuma saki wata mace ba tare da tuhumarta da wani abu ba, a bayan da aka kama ta jiya laraba lokacin sumame kan wani gida dake arewa da birnin Manchester.

Babban baturen ‘yan sanda na birnin Manchester da kewaye, Ian Hopkins, yace aiki ya buwayi jami’ansa a cikin ‘yan kwanakin nan amma kuma suna samun ci gaba a wannan binciken.

Ya fada yau alhamis cewa, “Ina son na tabbatarwa da al’umma cewa kame-kamen da muka yi suna da matukar muhimmanci. Binciken gidajen da muka yi kuma sun bankado wasu kayayyakin da muka yi imanin cewa suna da muhimmanci sosai ga wannan bincike.”

‘Yan sanda ba su bayar da wani bayani na irin alakar dake tsakanin mutanen da aka kama da kuma harin bam din ba.

A yau alhamis da safe, an yi zaman shiru na dan lokaci a birnin Manchester saboda jimamin wadanda suka rasa rayukansu a harin.

Mazauna birnin sun tattaru a makeken filin St. Ann, inda suka sadda kawunansu kasa a gaban wata rumfar furanni, da balam-balam da kendira da aka kafa don tunawa da mutane 22 da aka kashe a lokacin da Salman Abedi ya tada wani abin fashewa bayan wani taron kade-kade da raye-raye na wata shahararriyar mawakiyar Amurka da ake kira Ariana Grande.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG