koli na kungiyar tsaro ta NATO da aka gudanar a birnin Brussels. Shugabannin kungiyar sun hallara ne domin kaddamar da sabuwar shelkwatar kungiyar kawancen.
Trump ya ce "Ina Magana kai tsaye cewa membobin kungiyar kawancen NATO tilas ne su bada gudummuwarsu, su kuma sauke nauyin da ya rataya a wuyansu. Amma kasashe 23 cikin 28 har yanzu basu biyan abinda ya kamata su biya, da kuma abinda ya kamata su biya domin tsaronsu. Wannan ba adalci bane ga Amurkawa masu biyan haraji. Kuma ana bin kasasashen nan da dama makudan kudaden kudade na shekaru da dama kuma basu biya cikin shekarun da suka shige."
Trump ya kara da cewa, harin da aka kai a Manchester, alama ce ta zurfin keta da muke fuskanta da ta’addanci.
Tun farko PM Birtaniya, Theresa May tace zata yi bayyana rashin gamsuwa a tattaunawa da shugaba Trump dangane da kwarmatawa kafofin watsa labarai, bayanan binciken harin da aka kai Manchester da Amurka tayi.
Trump yace kwarmaton abin damuwa ne matuka ya kuma yi kira ga ma’aikatar shari’a ta gudanar da bincike.
Facebook Forum