An gurfanar da Alkaliya Rita Ofili-Ajumogobia, gaban baban kotun jahar Lagos, tare da wani babban Alkalin Najeriya Godwin Obla bisa zarginsu da laifin cin hanci da rashawa, wanda ake tuhumar Alkalan biyu da laifuka guda 30.
Sai dai kuma a yau din nan bayan da aka gurfanar da su baki dayansu sun musunta zargin da ake musu, inda kuma lauyansu ya gabatar da bukatar bada belinsu. Ya zuwa wannan lokaci dai Alkalin dake sauraron wannan shari’a Justice T. Oshodi, ya bayyana bukatar duba belin nasu kamar yadda lauyansu ya gabatar.
Wannan ne dai karo na biyu a kasar da hukumar EFCC take gurfanar da manyan alkalan Najeriya. tun da farko dai hukumar ta gurfanar da wani babban Alkalin kotun kolin Najeriya a birnin Abuja, wanda shima ake zarginsa da karbar na goro a lokacin yana bakin aiki, tare da ajiye wasu makurdan kudade a gidansa.
Duk da cewa wannan shari’a na gaban kotun ‘yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’yoyinsu game da matakan da hukumar EFCC ke dauka na yaki da cin hanci da rashawa.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5