Daruruwan Fulani makiyaya suka amsa gayyatar kungiyarsu kuma sun koka akan abun da suka kira wariyar da suke fuskanta a sahun dangi.
Matasalar da suka fuskanta ita ce ta baya bayan nan da ta biyo kazamin rikicin da ya faru a garin Bangi dake yankin Tawa.
Haruna Abarshi daya daga cikin shugabannin Fulanin yace wani lokacin dan fada ne kadan zai faru tsakaninsu da wani amma sai a farma gidajen Fulani a kashe yara da mata da tsoffi tare da kone gidajensu. Dalili ke nan Fulani suka ce yakamata su banbanta dan dumi da dan kubewa. Wanda yayi laifi a bari laifinsa ya cishi. Wanda kuma bai yi laifi ba kada abun ya shafeshi.
Yace mutane sun dauka abun da ya faru a Bangi kaman fada ne tsakanin mutanen garin da makiyaya alhali kuwa ba haka ba ne. Fada ne kawai ta kiyayya da kabilanci inda aka bi gidan Fulani daya bayan daya ana konewa.
Fulanin sun ce abun ya kaiga ko hari ma aka kai Nijar Fulani ake dorawa alhakinsa.
Malam Abubakar Jallo makiyayi da yake makwaftaka da iyaka da kasar Mali yace wasu na cewa Mujawo Bafillace ne. Yace da Fulani ya wuce cikin gari sai a daukeshi kamar dan Mujawo ne. Mujawo dai daga Mali suke. Malam Jallo yace su yi hattara kada abun da ya bata Mali ya bata tasu.
Kungiyar ta kira shugaban kasar Nijar da ya sa bakinsa a lamarin domin kubutar da Fulani daga kangin da suka fada. Sai dai kungiyar Fulanin tace ashirye take ta shigar da kara a kotun kasa da kasa idan samun sulhu ya cutura.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.