Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Malaman Kungiyar Tjjaniya Suka Taru A Yola Jihar Adamawa


Shaikh Dahiru Bauchi daya daga cikin shugaannin Kungiyar Tijjaniya da suka hallara a Yola
Shaikh Dahiru Bauchi daya daga cikin shugaannin Kungiyar Tijjaniya da suka hallara a Yola

Manyan malaman darikar Tijjaniya sun fito ne daga kasashe badan daban na duniya da suka hada da kasar Moroccoda Misra da Senegal da wasu kasashen da suka kai kimanin miliyan daya suka taru a Yola

Sama da al’umman Musulmi miliyan daya mabiya darikar Tijjaniya na ciki da wajen Najeriya ne suka gudanar da taron addu’o’I na musamman don kawo karshen matsalar Boko Haram da kuma matsalar tattalin arziki dake addabar Najeriya.

Yayin dai gudanar da wannan gangarumin taron addu’o’in dake da nasaba da maulidin Sheikh Ahmad Tijjani a karo na 288,mabiya darikan Tijjaniyar sun yi addu’ar samun nasara da dakarun Najeriya ke yi a yanzu a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram da kuma uwa uba matsalar kuncin rayuwar da ake fama da ita a yanzu.

Gwamnan Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo mai masaukin baki
Gwamnan Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo mai masaukin baki

Manyan Malaman na ciki da wajen Najeriya,wanda suka hada da Khalifan Sheikh Ahmad Tijjani a Nahiyar afrika Sheikh Muhammad Al-Kabir da Sheikh Aliyu Bil-Arabi,baya gas u Sheikh Dahiru Usman Bauchi daga Najeriya sun ce ,dole al’umman Najeriya su hada kansu don ciyar da kasar gaba.

A jawabinsa,babban mai masaukin baki,gwamnan jihar Adamawa wanda ke zama shugaban zakirai na Najeriya ,Sen.Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla ya yabawa shehunan Musuluncin bisa gudanar da taron addu’o’in samun zaman lafiyan.

Haka nan ,ba’a dai kammala taron ba,saida zakirai da muridai na ciki da wajen Najeriyan suka harraka.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:10 0:00

XS
SM
MD
LG