Jafaru isah tsohon gwamnan jihar Kaduna ne lokacin marigayi shugaba Janar Sani Abacha kuma dan takarar gwamnan jihar Kano a jamiyyar CPC a shekarar 2011 ya fada tarkon EFCC bisa zargin karban kudin sayen makamai daga ofishin tsohon mai bada shawarwari akan tsaro Kanar Sambo Dasuki.
Wanda shima yanzu haka yake tsare hannun hukumar tsaro masu sanye da farin kaya wato DSS.
Wannan dai ba zaizo da mamaki ba yadda shugaba Buhari ke jaddada yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar ba sani ba sabo.
Yawan kama yan jamiyyar adawa ciki harda kakakin jamiyyar PDP Oliseh Metuh ya sanya tababa ga masu hamayya da gwamnatin da ba mamaki awon gaba da Lawal Jafaru Isah zai sauya sukan da gwamnatin ke sha.
Ga abinda tsohon shugaban matasan jamiyyar PDP na jihar Yobe ke cewa gamre da wannan kamen da akeyi.
“Ba a kulle Ndime bane a kasar nan akwai wanda yayi zanga-zanga ne ?ba mutum daya da yayi tari don a barshi, sule Lamido an kulle shi Saminu Turaki an kulle shi, anje andauko dan gidan Baba Mai mangwaro an jefar dashi a CID wadannan duk an kama su, wa yayi zanga-zanga, addua ake yi.Amma abinda yake bada mamaki shine mutanen mu suna da laifi kuma yan arewa, mutum bai samu matsayi sai ya dauki dawainiyar wata kungiya ta kama surutu.
Ga Nasir Adamu El-Hikaya da Karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5