Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwaliya na biyan kudin sabulu wajen yaki da yan Boko Haram


Yan gudun hijira
Yan gudun hijira

Mallam Musa Zubairu mai nazarin harkokin tsaro a jami'ar kimiya da fasaha dake Kaduna, Nigeria yace sojojin Nigeria suna samun nasara akan yan Boko Haram

Mallam Musa Zubairu wani mai nazarin harkokin tsaro a kwalejin Kimiya da Fasaha dake Kaduna Nigeria, yace bisa bayanan da suke samu da kuma abubuwan da suke gani, kwaliya na biyan kudin sabulunta a yaki da yan Boko Haram

Yace idan aka lura hatta walwala na jama'a ta karu a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa. A saboda haka idan aka lura da wadannan abubuwa, za'a ga cewa gaskiya abubuwa kamar yadda aka yi niya ko kuma aka zata, kwaliya tana dan biyan kudin sabulun ta daidai gwargwado.

Akan cewa duk da ana samun nasara, yan Boko Haram suna ci gaba da kai hare hare, Mallam Musa Zubairu yace in ana maganar yaki da Boko Haram, ba'a yi masa kwasan karen mahaukaciya.

Yace idan aka tuna, akwai kanana hukumomi da yawa wadanda ada suke karkashin yan Boko Haram. Haka kuma ada ko daurin aure da wasu abubuwa. bai zai yiwu cikin kwanciyar hankali a jihohin arewa maso gabashin Nigeria ba.

Wasu yan gudun hijira, wadanda sojoji suka ceto daga yan Boko Haram
Wasu yan gudun hijira, wadanda sojoji suka ceto daga yan Boko Haram

Yanzu kuwa Alhamdullilahi ana samun saida. A saboda haka ne ya bada shawarar cewa ya kamata duk inda aka kwace, a kafa sansanin soja, domin hana yan Boko Haram komawa. A ganin su masu nazarin harkokin tsaro, kuskuren da ake yi shinr akan wuraren da aka kama, ba jami'an tsaro ko wani abu da zai nuna cewa an kama wannan wuri, ana kuma kokarin kare lafiyar mutanen da suke zaune a wadannan wurare.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG