Hukumar CCB Ta Dakatar Da Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Na Jihar Kano

Magaji Muhuyi

Hukumar Da’ar Jami’an Gwamnati ta CCB ta dakatar da Shugaban Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji, daga ofishinsa biyo bayan tuhume-tuhume 10 na cin hanci da aka shigar hukumar a ranar 16 ga Nuwamban shekarar da ta gabata.

WASHINGTON DC - Hukumar Da’ar Jami’an Gwamnati ta CCB ta dakatar da Shugaban Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji, daga ofishinsa biyo bayan tuhume-tuhume 10 na cin hanci da aka shigar hukumar a ranar 16 ga Nuwamban shekarar da ta gabata.

Dakatarwar na dauke ne cikin wani sanarwa da wadda take Magana da yawun hukumar, Veronica Kato, ta fitar a yau Alhamis a Abuja. A cewar Veronica, Hukumar ta dauki wannan mataki ne saboda kar yayi katsalanda a shari’ar da ake yi masa.

Kato ta kara da cewa “Da yake zartar da hukuncin, shugaban CCT, Mai shari’a Danladi Umar, ya tabbatar da cewa kotun tana da hurumin sauraron karar.”

Mai shari’a Umar ya jaddada cewa ba zai dace Magaji ya ci gaba da gudanar da ayyukansa a ofishinsa ba yayin da yake fuskantar shari’a.

An dage sauraran karar zuwa ranakun 7 da 8 ga Mayu, 2024. Ana sa ran a yayin wannan kararraki, masu gabatar da kara da masu kare wanda ake zargi za su bada bahasi su kuma gabatar da shaidu a gaban kotun.

A cewar Kato, an yanke hukuncin dakatar da Magaji ne don ganin bai yi katsalandan a shari’ar da ake yi masa ba.