Maniyyata Su Tanadi Naira Miliyan 4.5 - Hukumar Alhazan Najeriya

Hajj House NAHCON, Abuja

Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta nanata umurnin ajiye Naira miliyan 4.5 daga duk mai niyyar gudanar da aikin Hajjin 2024 gabanin karshen watan gobe.

ABUJA, NIGERIA - NAHCON ta ce ajiyar adadin kudin ya zama wajibi ne saboda tsadar dala da ake amfani da ita wajen biyan kujerar hajjin da sauran hidima ga alhazai.

Hajj House NAHCON Abuja

Sabon shugaban hukumar alhazan Alhaji Jalal Ahmad Arabi, ya nuna yanda ya rungumi sabon aikin don tabbatar da cewa aikin hajjin da ke tafe ya gudana ba tare da babbar dawainiya ga alhazai ba duk da yanda kujerar ka iya kara farashi.

Jalal Arabi ya ce sabon tsarin da hukumomin Saudiyya su ka kawo ya sa tattara kudin a kan lokaci don samawa alhazan VISA.

Jalal Ahmad Arabi – Chairman NAHCON

Alhaji Arabi wanda tsohon babban sakatare ne da ya yi aiki a fadar Aso Rock, ya ce shirin nan na adashen gata don zuwa hajji a tsawon shekaru na nan kamar yadda wasu fitattun kasashe ke yi.

Hakanan sabon shugaban da shugaba Tinubu ya nada bayan sauke Zikrullah Kunle Hassan ya ce akwai matakan sauya logar aiki da ya ke shirin kawowa.

Sheikh Bala Lau

Malaman Islama da ke fadakar da alhazai irin Sheikh Abdullahi Bala Lau na jan hankalin duk wanda ya samu damar tafiya hajji ya dage da ibada don samun babban rabo.

NAHCON kan kula da hukumomin alhazai na jihohi da kuma na jirgin yawo don yin zagi ga maniyyata da Najeriya kan samu kason kujeru 95,000 amma hakika tsadar dala kan sa zuwan sai mai tsananin rabo.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Alhazan Najeriya Ta Ce Maniyyata Su Tanadi Naira Miliyan 4.5 .mp3