Hukumar Alhazan Jihar Neja ta Hana Maniyattan Karamar Hukumar Bosso Zuwa Hajji

Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

Hukumar jin dadin alhazan jihar Neja ta tabbatar cewa wasu maniyatta su dari da ashirin daga karamar hukumar Bosso ba zasu tafi aikin hajjin bana ba sai dai idan karamar hukumarsu ta biya kudinsu kafin a gama jigilar alhazan jihar.

A wani taron manema labarai da shugaban hukumar alhazan tsohon babban alkalin jihar Jibril Ndajio yace sun dauki matakin ne saboda jami'in dake kula da harkokin alhazan karamar hukumar Alhaji Ahmed Bala Barkuta ya arce da nera miliyan talatin da biyu daga cikin kudin da alhazan suka biya.

Kawo yanzu ba'a san inda shi Alhaji Ahmed Bala Barkuta ya shiga ba sabili da haka maniyattan ba zasu tafi aikin hajjin ba har sai idan karamar hukumar Bosso ta biya kudin kafin lokaci ya kure. Mai shari'a Jibril Ndajio yace sai karamar hukumar ta biya kudin ko wanda ya kawo Alhaji Barakuta cewa shi ne zai tsaya wa maniyattan ya biya.

Da alama shi Alhaji Barkuta yayi layin zana domin babu wanda ya san inda yake. An tambayi sakataren mulkin karamar hukumar Bosson Alhaji Umar Sanda Aliyu wanda yace duk inda za'a samu mutum sun yi kokari basu sameshi ba. Abun tambaya nan shi ne yaya aka yi Barkuta ya samu tsabar kudin maimakon maniyatta su biya a bankuna.

A jihar Neja din ranar Lahadi mai zuwa za'a fara jigilar alhazan jihar.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Hukumar Alhazan Jihar Neja ta Hana Maniyattan Karamar Hukumar Bosso Zuwa Hajji - 2'58"