Jihohin da suka bar mata masu juna biyu zuwa aikin hajjin bana sune jihar Legas da Kogi da kuma Nasarawa, wadanda suka kai mata guda-guda masu ciki. Matar da aka kai daga Legas ta yi barin cikinta a Madina, amma matan da aka kai daga jihar Kogi da Nasarawa sun haihu, saboda cikinsu yakai lokacin haihuwa lokaicin da suke aikin hajji.
Shugaban kula da fannin lafiya na hukumar Alhazai Dakta Ibrahim Kana, ya ce anyi bita an kuma fadakar da cewa kada a bar mace mai juna biyu zuwa aikin hajji saboda wahalar aikin ka iya janyowa cikin ya zube ko matar ta shiga wani hali.
Dakta Ibrahim, yayi kira ga mata masu niyyar zuwa aikin hajji da su guji zuwa idan har suna da juna biyu, domin suna baiwa hukumar Alhazai wahala da kuma baiwa ‘kasa kunya.
A cewar Ambasada Umar Salisu, akwai takardu biyu da aka tanadar wadanda ko wanne guda zai iya fitar da jaririn da aka haifa zuwa kasarsa, na farko itace ayiwa jariri fasfo, idan kuma bai samu ba za a iya karbowa jariri takardar fita ta gaggawa daga ofishin jakadancin kasa.
Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5