Saudiyya Ta Kakkabo Rokar 'Yan Tawayen Houthi

Dogayen Gine-gine a Riyadh

Dogayen Gine-gine a Riyadh

A yau Talata ‘yan tawayen Houthi a Yemen sun harba makami mai linzami kan babban birnin Saudi Arabia, inda suke cewa sun auna shi ne kan fadar Yamama a birnin na Riyadh.

Dakarun hadin gwiwa da Saudiyya ke jagoranta da ke fafatawa da ‘yan tawayen Houthi na kusan shekaru uku sun ce sun kakkabo wannan makami mai linzami daga sama, yayin da kafofin yada labarai na Sa'udiyya suke bayyana cewa babu wanda lamarin ya ji wa rauni.

Harin makamin mai linzami da aka kai a watan Nuwamba ya sa dakarun hadin gwiwa da Saudi ke jagoranta kulle hanyoyin shiga Yemen na saukar jiragen sama, da na ruwa da kuma na kasa na takaitaccen lokaci. Saudiya ta ce matakan sun zama wajibi domin tabbatar da cewa Iran bata ba ‘yan tawayen Houthi makamai ba, ta kara da cewa ta yi la’akari da matakan na Iran, a matsayin “takalar yaki”.

Iran na marawa ‘yan tawaye baya amma ta musanta basu makamai. Iran ta kuma zargi Saudiyya akan amfani da karfin soji a Yeman lamarin da ta kira “take marasa karfi a yankin”.

‘Yan tawayen Houthi sun kwace Sanaa, babban birnin kasar Yemen a karshen shekarar 2014, lamarin da ya tilasatawa shugaban kasar Abdu Rabu Mansour Hadi, tserewa zuwa kasar Saudiyya, dakarun hadin gwiwa da Saudi ke jagoranta suka mayar da martani domin kare gwamnatin Hadi, rikicin da ya jefa fararen hular kasar cikin mummunar matsala ta jinkai.