Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kunar Bakin Wake Sun Barraka Wata Majami'a A Pakistan


Wasu mata lokacin addu'a bayan hari a wani cocin Pakistan
Wasu mata lokacin addu'a bayan hari a wani cocin Pakistan

Tsirarun Kiristan kasar Pakistan sun sake dandanawa, bayan da wasu 'yan kunar bakin wake su ka yi kukan kura su ka dumfari wani coci da jami'an tsaro ke gadinsa a birnin Quetta na kasar Pakistan, su ka tarwatsa kansu, su ka kashe masu ibada akalla 9. Tuni aka shiga addu'o'i da daukar karin matakan tsaro.

Jiya Lahadi ‘yan kunar bakin wake akalla biyu, masu dauke da manyan makamai sun abka ma wata majami’a mai cike da mutane a birnin Quetta, wanda ke kudu masu yammacin Pakistan, su ka kashe masu ibada akalla 9 daga cikin al’ummar Kirista tsiraru.

Jami’ai da likitoci sun ce yara kanana da mata na cikin wadanda harin da aka kai kan Majami’ar Bethel Memorial Methodist wanda ke yankin da ke cike da tsaro a birnin.

Babban jami’in ‘yan sanda, Sufeto-Janar Mu’azzam Ansari, ya gaya ma manema labarai cewa na uku daga cikin maharin ya gudu zuwa wata unguwar da ke kusa lokacin da ake musayar wuta, kuma ana kan shirin farauto shi.

Ansari ya ce da ba don ‘yan sandan da ke tsaro sun gaggauta daukar matakin hana maharan shiga majami’ar ba da mutane da dama sun mutu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG