Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Hau Kujerar Na-ki Kan Kudurin Birnin Kudus


Masu zanga zanga a Masar
Masu zanga zanga a Masar

Duk da kasashen Musulmi suna ta Allah wadai akan hukuncin da Amurka ta yanke na maida Qudus babban birnin Isra'ila, Amurkan ta ce babu gudu kuma babu ja da baya.

Amurka ta hau kujarar na-ki wajen kada kuri'a kan wani kuduri da ya so ya yi Allah wadai da matsayar da ta dauka na ayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

Shugaba Donald Trump ya ayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila a farkon watannan, lamarin da ya janyo suka daga sassan duniya.

Amurka na daya daga cikin mambobi biyar na kwamitin da ke da kujera ta dindindin a kwamitin.

Hakan kuma na nufin tana da damar hawa kujerar na-ki kan duk wani abu da ba ta amince da shi ba.

Sauran mambobin kwamitin su 14 sun zabi daftarin wanda kasar Masar ta tsara.

Kalaman da ke cikin daftarin, sun yi Allah wadai tare da nuna takaici kan sanarwar da shugaba Trump ya yi a farkon watannan.

Trump ya kuma nuna aniyar Amurka ta fara shirye-shiryen mayar da ofishin Jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa birnin na Kudus.

Shi dai Trump ya ce sanarwar da ya yi “gaskiya ce ya fada karara" kan wani batu da ya zama zahiri.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG