Hotunan 'Yan Boko Haram da Suka Tuba a Nijar

Mayakan Boko Haram da suka tuba a cibiyar da ake horas dasu a Diffa, Nijar, ranar 17 ga watan Afirilu, 2017 (VOA/Nicolas Pinault)

Wurin da ake kulawa da 'yan Boko Haram a Diffa, Nijar, ranar 17 ga watan Afirilu, 2017 (VOA/Nicolas Pinault)

Wasu mayakan Boko Haram a Diffa, Nijar, ranar 17 ga watan Afirilu, 2017 (VOA/Nicolas Pinault)

Wasu mayakan  Boko Haram da suka tuba a cikin gidan da suke a Diffa, Nijar, ranar 17 ga watan Afirilu 2017 (VOA/Nicolas Pinault)

Daya daga cikin ginin cibiyar horas da 'yan Boko Haram, Diffa, Nijar, ranar 17 ga watan Afirilu 2017 (VOA/Nicolas Pinault)

Wasu tsoffin mayakan Boko Haram da suka tuba a Diffa, Nijar,  17 ga watan Afirilu, 2017 (VOA/Nicolas Pinault)

Ibrahim Malam Toura, dan shekara 14 da 'yan Boko Haram suka sace tun yana dan yaro karami shi ma yana  Diffa, Nijar, 17 ga watan Afirilu 2017 (VOA/Nicolas Pinault)

Malam Boucar Adam, da malamin makaranta ne kafin ya shiga kungiyar Boko Haram. Yana yi kamar bai taba  yin kisa ba ko aikata wani mugun aiki yayinda yake yiwa kungiyar aiki a matsayin likita na bogi. Ya bar kungiyar bayan da ya gane cewa addinin Islama addini ne da yake koyas da zaman lafiya ba kashe mutane ba. Yana  Diffa, Nijar ranar 17 ga watan Afirilu 2017 (VOA/Nicolas Pinault)

Moustapha Aboubacar, tsohon mayakin Boko Haram, a Diffa, Nijar, ranar 17 ga watan Afirilu 2017 (VOA/Nicolas Pinault)

Tsohon mayakin Boko Haram yana wanke kayansa a Diffa, Nijar, ranar 17 ga watan Afirilu 2017 (VOA/Nicolas Pinault)

Wasu kayan da tsoffin mayakan Boko Haram ke sawa a  Diffa, Nijar, ranar 17 ga watan Afirilu 2017 (VOA/Nicolas Pinault)

Wani tsohon mayakin Boko Haram yana wasa da dan yaro a Diffa, Nijar, ranar 17 ga watan Afirilu 2017 (VOA/Nicolas Pinault)

Mata suna tadi a  Diffa, (VOA/Nicolas Pinault)

Yarinya tana diban ruwa a cibiyar horas da 'yan Boko Haram da suka tuba a Diffa (VOA/Nicolas Pinault)

Yara suna wasa (VOA/Nicolas Pinault)

Yara suna gaban ginin cibiyar horas da 'yan Boko Haram da suka tuba (VOA/Nicolas Pinault)

Titin shiga gabashin birnin Diffa (VOA/Nicolas Pinault)

Yayinda da rundunar sojojin hadin gwuiwar kasashen dake fafatawa da Boko Haram ke cigaba da kakkabe 'yan ta'addan a kan iyakokin Nijar da Najeriya, har zuwa Tafkin Chadi, an bude cibiyar horas da 'yan Boko Haram da suka mika kai tun watan Disamban bara a Diffa. A wannan cibiyar ce wakilin Muryar Amurka a Nijar Nicolas Pinault ya gamu da wasu 'yan Boko Haram da suka tuba