Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Amurka A Shirye Take Ta Yaki Koriya Ta Arewa?


Masu fashin baki sun ce an samu bayanai masu karo da juna, ko kuma na karya, dangane da jirgin yakin ruwan Amurka da hukumomin kasar suka ce sun tura zuwa tekun Korea mai suna “armada”.

Yanzu haka wannan lamarin ya haifar da shakku kan barazanar da Amurkan ke yi na cewa za ta yi amfani da karfin soji akan Korea ta Arewa.
A farkon watan Aprilu, Fadar White House da rundunar sojin Amurka dake yankin Pacific sun ce jirgin yakin ruwan Amurka mai suna USS Carl Vinson wanda jiragen yakin sama ke sauka a kansa, ya nufi yankin Tekun Japan, domin kasancewa cikin shirin maida martani idan Korea ta Arewa ta takali Amurkan.
Sai dai jirgin ruwan, yana can a kudancin tekun India, inda ake gudanar da atisaye a yankin Australia.
A jiya Talata, Kwamandan rundunar sojin Amurka a yankin Pacific, ta ce dakarun da aka tanada za su kai farmaki sun doshi yammacin yankin tekun Pacific.
“Idan har aka yi barazanar kai musu hari, aka kuma gano barazanar karya ce, hakan zai disashe duk wata manufa da ake da ita akan Korea ta arewan", a cewari Joel Wit, kwararre a fannin huldar kasa da kasa.
A ranar 12 ga watan Afirilu shugaba Donald Trump ya fada da babbar murya cewa Amurka ta tura jirgin yakin ruwan Amurka na Armada zuwa yankin Korea.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG