Babbar shugabar Hong Kong, Carrie Lam, ta ce, gwamnati za ta fitar da wani kudurin dokar hana fita wanda ya haddasa zanga - zanga ta kusan watanni uku don nuna adawa.
A cikin wani sakon bidiyo da ta fitar a yau Laraba daga ofishin nata, Lam, ta ce, ta janye kudirin, wanda ada zai ba da damar a tura wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka zuwa kasar China don fuskantar hukunci a kotuna, wanda Jam'iyyar Kwaminis mai mulki ke jagoranta, "don kawar da damuwar jama'a."
Amma tsohon dan gwagwarmayar demokiradiyya na Hong Kong, Joshua Wong, ya fada wa manema labarai, bayan Lam ta sanar da shawarar janye dokar, cewa" matakin da ta dauka bai isa ba, kuma yazo a makare."
Sanarwar ta yau Laraba na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da aka ji Lam na cewa, a cikin wani faifan sauti, wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya samu, inda take fadawa shugabannin kasuwannin Hong Kong cewa ta haddasa "mummunan rikici" lokacin da ta gabatar da wata doka kan batun, abinda ya kara haifar da zanga-zangar.