Kwararru sun ce, guguwar na kara zama mai karfin gaske, za ta kuma rabi jihohin Florida da Goergia a daren Talata zuwa wayewar garin Laraba, sannan za ta zubar da ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohin North Carolina da South Carolina dauke da guguwa mai karfin gaske.
A cewar gwamnan jihar ta North Carolina, Roy Cooper, “lura da cewa ana fargabar guguwar za ta kara saurin tafiyarta, lokacin da ake da shi na kimtsawa na korewa.”
Guguwar wacce tuni ta sauka kai-tsaye akan yankin Bahamas, ta lalata akalla gidaje dubu-goma-sha-uku a kiyasin farko da aka yi.
Facebook Forum