Hira Da Dr. Sambo Sadiku Kan Raguwar Mutuwar Kananan Yara A Nijar Kashi Na Uku

Uwa da jariri

A kammala bayanin hirar da Dr Sambo Sadiku ya yi da wakilin sashen Hausa Abdoulaye Mamman Ahmadu kan raguwar mutuwar kananan yara a jamhuriyar Nijar, Dr Sadiku ya ce ko da yake an sami raguwar mutuwar kananan yara a Nijar amma har yanzu Ana ci gaba da samun mace macen jarirai. Ya ce dalilin da ya sa haka shine rashin nazari akan jarirai.
A kammala bayanin hirar da Dr Sambo Sadiku ya yi da wakilin sashen Hausa Abdoulaye Mamman Ahmadu kan raguwar mutuwar kananan yara a jamhuriyar Nijar, Dr Sadiku ya ce ko da yake an sami raguwar mutuwar kananan yara a Nijar amma har yanzu Ana ci gaba da samun mace macen jarirai. Ya ce dalilin da ya sa haka shine rashin nazari akan jarirai. Da shike an maida hankali kan yara da suka dan yi wayo, ba a kula da sababbin haihuwa ba.

Ban da haka kuma, inji Dr. Sadiku, da akwai mata da sukan haihu a gida. Wanan yakan kawo damuwa tunda ba za a san yaro yana da damuwa ba har sai lokaci ya kure, kuma kafin a kawo shi asibiti ba abin da za a iya yi mishi. Bayan haka, Dr. Sadiku yace ya kamata mata su rika zuwa asibiti domin awo. Zuwa asibiti domin awo, da haihuwa a asibiti wajen likita, sune za su taimaka wajen hana mutuwan jarirai.

Dr Sadiku ya ce za su ci gaba da yin aiki domin rage yawan yara da suke mutuwa ko wace shekara. Ya ce ba su daina aiki domin ganin sun ci nasara wajen rage yawan mutuwan yara ba.

Ya kuma kara da cewa, za su fara yin aiki wajen taimakon mata masu ciki, ko kuma mata da suka kai shekarun yin ciki. Anan za su taimaki mata wajen kula da ciki da kuma bada rata tsakanin haihuwa, saboda idan akayi haka, za a ba sabon haihuwa lokacin yin kwari da karfi.