Babban jami'in kiwon lafiya ya yi juyayin rasa ma'aikatan kiwon lafiya 13 da aka kashe tsakanin Kano da Borno da Yobe. Ya ce jami'an kiwon lafiya har yanzu suna iya bakin kokarinsu wurin taimakawa majinyata. Yace ana yabawa wadanda suka yi aikinsu tsakaninsu da Allah haka ma ana hukumta wadanda suka yiwa aikinsu rikon sakainar kashi, musamman idan sun wulakanta marasa lafiya.
Dr Ahmed Gana daraktan matakin farko na kiwon lafiya dake jihar Gombe daya daga cikin jihohin dake cikin dokar ta baci ya bayyana yadda aka rage muruwar mata yayin haihuwa.Ya ce yawan 'yan Najeriya bai fi kashi uku ba a 'yawan al'ummar duniya amma Najeriya ce ke da kashi goma cikin dari na duk matan dake mutuwa lokacin haihuwa a duk fadin duniya. A cikin Najeriya lamarin ya fi kamari a jihohin arewa maso gabas. Mata musamman na kauyuka suna mutuwa domin rashin hanyoyin da zasu samu su fito zuwa inda za'a kula da su. Ya ce idan kuma aka samu aka kai asibiti to samun kula kuma ya kan zama da matsala. Ya ce idan aka samu kananan asibitoci a sako sako zasu taimaka wajen inganta samun lafiya. Ya ce idan mace ta dauki ciki ya kamata ta samu ta ziyarci asibiti a kalla kamar sau hudu.
Idan ma mace bata samu zuwa asibita ba sau hudu to ace yayin da ta samu juna biyu ta je asibiti inda za'a bata magani da zata rika sha har ta kai lokacin haihuwa kafin ta je.
Mata masu juna juna biyu ana kula dasu kyauta sai dai yajin aiki da wasu likitoci kan yi ko kuma kungiyar likitocin na wahalar da jama'a da jefa majinyata cikin halin kakanikayi. Masu hannu da shuni kuma sai su ruga asibitin dake zaman kansu wadanda yawanci mallakar likitocin dake yajin aiki ne ko kuma suna aiki a cikinsu. A gaskiya asibitocin alumma ba kasafai suke aiki ba.
Ga Nasiru Adamu El-Hikaya da bayani.