Hezbollah Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Yakar Isra’ila Bayan Kisan Nasrallah

Sheikh Naim Qassem (Foto: Mohamed Azakir/REUTERS)

Shugaban Hezbollah na riko ya sha alwashin ci gaba da yakar Isra’ila sannan ya bayyana cewar a shirye kungiyar take ta shafe dogon zango tana yaki duk kuwa da cewar an hallaka manyan kwamandojinta, ciki harda jagoranta, Hassan Nasrallah.

Duk da mummunan koma bayan da Hizbullahi ta samu a makonnin baya-bayan nan, shugabanta na riko Naim Kassem ya bayyana a cikin sanarwar da aka yada ta kafar talabijin cewar idan har Isra’ila ta yanke shawarar kaddamar da yaki ta kasa, a shirye mayakan kungiyar suke, inda yace an riga an maye gurbin kwamandojin da ta hallaka.

Lebanon 30 Satumba 2024. (Foto: Jim Urquhart/REUTERS)

Kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ba za ta bata lokaci ba wajen zabin mutumin da zai gaji jagoranta da aka hallaka Hassan Nasrallah sannan zata cigaba da yakar Isra’ila, a cewar mataimakin shugaban kungiyar da Iran ke marawa baya Naim Qassem a yau Litinin.

Ya yi bayanin ne a jawabin da aka yada ta kafar talabijin, karon farko ke nan da wani jami’in Hezbullah ya bayyana tun bayan kisan da wani harin Isra’ila ya yiwa Nasrallah a yankin kudancin babban birnin Lebanon a Juma’ar da ta gabata.

Hare-haren Isra’ila ta sama sun hallaka Nasrallah tare da wasu manyan kwamandoji da jami’ansa 6 a kwanaki 10 da suka gabata, kuma ta kai hari kan wuraren da rundunar sojin ta bayyana da mallakin Hezbullah ne a sassan Lebanon da dama.

Hassan Nasrallah

Cikin makwani 2 da suka gabata an hallaka fiye da mutane dubu a Lebanon, kusan 1 bisa 4 mata da kananan yara, a cewar ma’aikatar lafiyar kasar.

-Reuters