Kakin hedkwatar rundunar tsaron kasar, Manjo Janar Jimmy Akpor cikin wata sanarwar da ya sanyawa hanu yace baki dayan mayakan kasar suna biyayya kuma za su ci gaba da mika wuya ga tsarin demokradiyya kamar dai yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.
Janaral Jimmy yace ai ba yadda za a ma ce akwai wani batun juyin mulki a halin yanzu, kasancewa, sojin ne suka mikawa fararen hular mulki kuma suka yi ta kare tsarin don haka ba yadda a yanzu kuma za su yi kasadar yin kutse a sha'anin mulkin.
Tunda farko dai tsohon ministan harkokin sufurin jiragen saman kasar kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulki Chief Femi Fani Kayode ya zargi mayakan kasar da kitibibin kitsa yin juyin mulkin.
Ku Duba Wannan Ma Shugaba Buhari Na Da Karamci Da Yafiya Ga Masu Sukar Sa - Femi AdeshinaSai dai duk da hedkwatar tsaron kasar ta musanta batun a cewar masanin kimiyyar siyasa Dr, Farouk BB Farouk na jami'ar Abuja zargin juyin mulki fa babbar magana ce, don haka dolene a kaddamar da bincike don sanin ainihin me ke faruwa,
Kazalika shima masanin tsaro Dr Kabiru Adamu yace ire iren ababen dake faruwa a Najeriya na rashin tsaro da ma tabarbarewarsa da kuma gazawa irin na 'yan siyasa sune suka haddasa juyin mulki a wasu kasashen dake kewaye da Najeriya, don haka dolene a baiwa wannan magana muhimmanci.