Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Na Koma Jam’iyyar APC – Fani-Kayode


Buhari, hagu, Fani-Kayode, dama a fadar Aso Rock (Facebook/Femi Adesina)
Buhari, hagu, Fani-Kayode, dama a fadar Aso Rock (Facebook/Femi Adesina)

Fani-Kayode ya kasance daya daga cikin masu sukar lamirin gwamnatin APC mai mulki kan yadda take tafiyar da sha'anin mulkinta.

Tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, Femi Fani-Kayode ya koma jam’iyyar APC mai mulki, in ji kakakin shugaba Buhari, Femi Adesina.

Shugaban kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar ta APC kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ne ya gabatar da Fani-Kayado ga shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Alhamis.

Rahotanni sun ruwaito Fani-Kayado yana cewa Allah ne ya karkata hankalinsa ya koma kan jam’iyyar, yana mai cewa ya yi hakan ne don ya taimaka wajen hadin kan kasa kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Fani-Kayode, wanda mamba ne da a jam’iyyar ta APC, ya fice daga jam’iyyar a shekarar 2014.

A cewar tsohon ministan, ya taka muhimmiyar rawa wajen komarwar wasu gwamnonin PDP zuwa jam’iyyar mai mulki.

A baya-bayan nan masu lura da al’amuran siyasa sun yi ta sharhi kan yadda tsohon ministan yake rabar manyan jami’an gwamnati da gwamnonin jam’iyyar ta APC mai mulki.

A watan Agusta Fani-Kayode, ya halarci daurin auren dan shugaba Buhari, Yusuf Buhari a Kano, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.

A da, Fani-Kayode ya kasance na gaba-gaba a jerin masu yawan sukar lamirin gwamnatin Buhari kan yadda take tafiyar da sha’anin mulkinta.

Ya sha wallafa cewa ba zai taba komawa jam’iyyar ta APC ba, inda har rahotanni suka ce ya ce gara yam utu da ya koma jam’iyyar.



Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG