Hedkwatar Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ta Fara Wani Shirin Horas Da Kwamandojin Rundunoninta

Hedkwatar Rundunar Yansandan Najeriya

Hedkwatar rundunar 'yan sandan Najeriya ta fara wani shirin horas da kwamandojin rundunoninta na kwantar da tarzoma su saba'in da tara don tabbatar da zama cikin damara kafin lokaci da bayan babban zaben gama gari na kasa da za'ayi cikin wannan shekara.

Horon da za a shafe makonni biyu ana yi da kuma ake sa ran zai yi tasiri wajen samar da tsaro yayin zaben, kazalika za a kuma nakalci sarrafa sabbin na'urorin kwantar da tarzoma na zamani da kuma kwarewa wajen tunkarar duk wani nau'in kwanton bauna, sarrafa makamai da dai sauran ababen dake da alaka da tsaro.

Hedkwatar Rundunar Yansandan Najeriya

Da yake jawabi ga kwamandojin, babban sufetan 'Yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya horesu da su yi kyakkyawan amfani da wannan horo da aka basu don tabbatar da kokarin samar da cikakken tsaron da zai kai ga samun zaben gaskiya mai cike da adalci a kasar nan.

Daga bisani Babban baturen 'yan sandan ya kuma gana da wakilan ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake sa ido kan miyagun laifuka da miyagun kwayoyi wato UNODC inda suka tattauna yiwuwar kawancen karfafa manufofin ganin kyautatuwar da'a da gaskiya cikin sha'anin harkar 'yan sanda.

Hedkwatar Rundunar Yansandan Najeriya

Sufeta janar din ya nanata kudirinsa na yin aiki kafada da kafada da duk sassan dake hankoron ganin an kyautata yanayin tsarin aikin 'yan sanda.

Babban zaben Najeriya dai da kwararru suka yi hasashen ka iya haduwa da cikas musamman ganin yadda 'yan ta'adda suka kara matsa kaimi wajen tafka aika aika a dai dai lokacin da zaben ke kara matsowa, ana ganin ka iya haduwa da cikas, lamarin da jami'an tsaro ke cewa sun shirya.

Ko a makon jiya sai da hukumar zaben kasar ta ce lalle akwai yiwuwar dage zaben ma baki daya muddin sha'anin tsaron dake kara sukurkucewa bai inganta ba, kalaman da bai yiwa gwamnatin kasar dadi ba, inda ministan labaru na kasar Lai Mohammed ya yi watsi da batun.