Bayanai daga hukumar ba da agaji gaggawa sun nuna cewa, ba a kada kararrawar gargadi ba kafin mutane su fara tserewa don tsira da rayukansu yayin da wata wutar daji ta shi a yankin Maui a Hawaii wacce ta halaka mutum 55.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa a maimakon kada kararrawa, sai jami’ai suka tura sakonnin tes zuwa wayoyin jama’ar yankin.
Kazalika an aike da sakonni ga kafafen talbijin da rediyo.
Shi dai yankin na Hawaii da ke Amurka, kan yi tunkaho da kasancewa yanki da ya fi ingantattun hanyoyin kare aukuwar hadurra a duniya.
Sai dai da yawa daga cikin shaidu da aka zanta da su a ranar Alhamis, sun ce ba su ji kararrawar gargadi ba ko wani abu da zai ba su isasshen lokacin da za su tsere.
Jama’ar yankin sun kara da cewa, ba su ankara da cewa akwai damuwa ba, sai bayan da suka ga tashin wutar.
Wannan wutar daji ita ce ibtila'i mafi muni da ta auku a yankin na Hawaii tun bayan hadarin tsunami da ya faru a 1960 wanda ya halaka mutum 61.
Gwamnan jihar ta Hawaii Josh Green ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar adadin mutanen da suka mutu ya karu yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan ceto.