Hausawa Na Korafi Kan Rashin Ba Su Damar Neman Mukaman Siyasa A Jihar Kwara

Gwamnan Jihar Kwara AbdulRazaq AbdulRahman

Gwamnatin jihar Kwaran dai ta ce tana damawa da kowa a jihar sai dai watakila Hausawan ne ke yin baya-baya a shiga harkokin siyasar jihar.

Al’ummar Hausawa dake zaune a jihar Kwaran Nigeria sun nuna damuwa matuka a kan rashin basu damar tsayawa takarar neman mukamin Siyasa a jihar.

Jihar Kwaran dai na da tarin kabilar Hausawa da suka je domin Harkokin kasuwanci da sauransu.

Malam Ahmed Tahir shine Sakataren kungiyar Hausawa magoya bayan Jam’iyyar APC a jihar Kwara ya yi karin haske a kan wannan matsala da suke fuskanta.

Ya ce “babbar bukatar mu itace idan takara ta zo a bamu dama mu shiga takara kamar yanda kowane dan kasa yake shiga takara kuma a mara muna baya a gwamnatance saboda mu kai ga wani babban matsayi na siyasa a jihar.” A halin Yanzu babu wani ba-Haushe da aka bashi daman tsayawa neman mukamin siyasa.

Suma dai wasu daga cikin shugabannin Hausawan na birnin Ilorin sun yi karin haske da cewa wasu jihohin a kudu suna samun wannan dama amma jihar Kwara dake zaman yankin Arewa sun kasa samun irin wannan dama.

Gwamnatin jihar Kwaran dai ta ce tana damawa da kowa a jihar sai dai watakila Hausawan ne ke yin baya-baya a shiga harkokin siyasar jihar domin a dama dasu, inji mai baiwa Gwamnan jihar Kwaran shawara a kan harkokin Hausawa Malam Isah Isyaka Jega.

A yanzu dai Gwamnan Jihar Kwaran Abdurrahman Abdurrazak na neman wa’adi na biyu ne a karkakshin inuwar jam’iyyar APC, al’amarin da masu sharhin siyasar Kwaran ke ganin akwai bukatar ganin Gwamnan ya maida hankali wajan dinke ‘yar tankiyar dake tsakaninsa da yankin kudancin jihar kwaran, yankin da Ministan Labaran Nigeria Lai Muhammad ya fito.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga birnin Ilorin.

Your browser doesn’t support HTML5

Hausawa Na Korafi A Kan Rashin Basu Daman Neman Mukaman Siyasa A Jihar Kwara.MP3