Hauhawar Farashin Kayayyaki Ta Ragu Zuwa Kaso 32.15 Cikin 100 A Watan Agusta -NBS

  • VOA Hausa

Kayan masarufi a wata kasuwar Abuja a Najeriya

A cewar alkaluman kididdigar farashin sayen kayayyaki da NBS ta fitar, ma’aunin auna jumlar hauhawar farashin ya ragu zuwa kaso 32.15 cikin 100 a watan Agustan da ya gabata.

A yau Litinin, Hukumar Kididdigar Najeriya (NBS) ta bayyana cewa an samu raguwar hauhawar farashin kayayyakin masarufi a Najeriya tsawon watanni 2 a jere, daga kaso 34.19 a watan Yuni zuwa kaso 33.40 a watan Yuli, da kuma yanzu kaso 32.15 cikin 100 a watan Agustan da ya gabata.

A cewar alkaluman kididdigar farashin sayen kayayyaki da NBS ta fitar, ma’aunin auna jumlar hauhawar farashin ya ragu zuwa kaso 32.15 cikin 100 a watan Agustan da ya gabata, yayin da na hauhawar farashin kayan abinci ya tsaya a kan kaso 37.52 cikin 100 a watan na Agusta.

NBS ta kara da cewa hauhawar farashin kayan abinci a watan Agustan da ya gabata ya tsaya a kan kaso 37.52 cikin 100 a bisa ma’aunin gane bambancin farashi tsakani shekara da wacce ta ragayeta, inda ta karu da kaso 8.18 cikin 100 a kan yadda yake a watan Agustan shekarar 2023 (kaso 29.34 cikin 100).

Ku Duba Wannan Ma Hauhawar Farashin Kayayyaki Ta Ragu A Watan Yuli - NBS